Hukumar gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da naɗin Daniel Ogunmodede a matsayin sabon babban kocin ƙungiyar domin jagorantar ta a kakar wasan firimiyar Najeriya ta 2026/2027.

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ƙungiyar ya fitar a ranar Juma'a, an bayyana cewa Ogunmodede, wanda aka fi sani da "Ijaball", zai jagoranci harkokin fasaha na ƙungiyar yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar sabuwar kakar wasa.

Sanarwar ta ce naɗin nasa wani ɓangare ne na shirin sake fasalin ƙungiyar domin inganta bajintarta a gasannin cikin gida da kuma na nahiyar Afirka.

Ogunmodede, tsohon kocin Remo Stars, ya maye gurbin Muhammad Babaganaru a matsayin shugaban masu horar da Kano Pillars.

Kano Pillars ta kammala kakar wasan da ta gabata a matsayi na 15 a teburin gasar, bayan ta tara maki 48 daga wasanni 38, kuma na fatan sabon kocin zai taimaka wajen dawo da ƙungiyar cikin manyan masu fafatawa a gasar.