Takaddama ta ɓarke tsakanin gwamnatin Najeriya da jam’iyyun adawa bayan wani rahoto ya haifar da ce-ce-ku-ce kan yadda aka kashe wasu kuɗaɗe da kuma yadda gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi.
Jam’iyyun adawa sun yi zargin cewa akwai alamun rashin gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, musamman yayin da ake tunkarar zaɓe. Sun danganta hakan da wani rahoto da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar, wanda ya yi nuni da cewa wasu kashe-kuɗaɗe da suka kai kusan tiriliyan 8.8 naira ba su shiga cikin kasafin kuɗin gwamnati ba.
Rahoton ya nuna cewa waɗannan kashe-kuɗaɗen sun kai kusan kashi biyu cikin ɗari na jimillar tattalin arzikin ƙasar (GDP), lamarin da ya jawo tambayoyi daga masu sukar gwamnati.
Sai dai Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta yi watsi da zarge-zargen, tana mai cewa dukkan kuɗaɗen da aka kashe an yi su ne bisa tanade-tanaden doka kuma cikin tsarin da ya dace. Ma’aikatar ta kuma ƙalubalanci masu zargin gwamnati da su gabatar da hujjoji idan suna da su, maimakon yin zarge-zarge marasa tushe.
A gefe guda, alkaluma sun nuna cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ci gaba da karɓar bashi daga cibiyoyin ba da lamuni na ƙasa da ƙasa, ciki har da Bankin Duniya, domin tallafa wa shirye-shiryen ci gaban ƙasa da kuma gyaran tattalin arziki.
Masana tattalin arziki na cewa, duk da ƙarin kuɗaɗen shiga da gwamnati ke samu daga wasu sassa bayan sauye-sauyen manufofi, har yanzu miliyoyin 'yan Najeriya na fuskantar matsin rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki, abin da ke ci gaba da jefa tattalin arzikin ƙasar cikin ƙalubale.
Rahoton IMF da martanin gwamnatin sun ƙara rura wutar muhawara kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen gwamnati da kuma tasirin manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu ga rayuwar al'umma.