Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff, kan ikirarinsa cewa Peter Obi ba shi da ƙarfin samun goyon baya a Arewacin Najeriya.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce kalaman Sheriff ba su yi daidai da hakikanin siyasar Arewa ba, yana mai tunatar da cewa Obi ya samu kusan ƙuri'u miliyan 2.8 a Arewa a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata.
Ya kuma ce matsalolin tattalin arziki da tsaro da ake fuskanta, tare da abin da ya kira gazawar gwamnatin APC, sun ƙara wa haɗakar tikitin OK ƙarfi a Arewa.
Kwankwaso ya musanta zargin Sheriff cewa al'ummar Kano ba za su goyi bayan Obi ba, yana mai cewa mutanen Kano suna mara wa duk ɗan takarar da tafiyar Kwankwasiyya ta amince da shi baya ba tare da la'akari da ƙabila ko yanki ba.
Ya kuma buƙaci Sheriff ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro da ke addabar Jihar Borno, maimakon yin kalaman da zai iya raba kan al'umma.